text
stringlengths 101
6.99k
| language
stringclasses 1
value |
---|---|
Image caption Joseph Yobo shi ne kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da za su Afrika ta Kudu | ha |
Najeriya ta dauki 'yan wasa shida dake wasa a cikin gida, a jerin sunayen 'yan wasa 23 da ke tawagar kasar, da za su je Africa ta Kudu. | ha |
Kasar dai ta kwashe sama da shekaru ashirin rabonta da ta sanya 'yan wasan cikin gida a tawagar gasar cin kofin nahiyar Afrika. | ha |
Mai horar da 'yan wasan, Stephen Keshi ya ce " sun cancanci shiga, kuma ina ganin wannan tamkar wata dama ce da 'yan wasan cikin gidan zasu nuna cewa, ba a yi zaben tumun dare ba." | ha |
An dai cire sunanyen dan wasan gaba dake zaune a Amurka, Bright Dike da kuma dan wasan tsakiya Raheem Lawal wanda ke wasa a Turkiyya, a tawagar Najeriyar. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka | ha |
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma jigo a jam'iyyar DPP ya yanki katin shiga jam'iyyar ACN a mazabarsa ta Bafarawa dake jihar Sakkwato. | ha |
Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce ya yanke wannan hukunci ne domin mutunta yarjejeniyar da yace an cimma a baya da wasu 'yan siyasa na shiga wannan jam'iyya ta ACN. | ha |
Sai dai kuma shigar tasa jam'iyyar ACN ta bar baya da kura domin wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar sun ce suna nan Daram a cikin jam'iyyar DPP. | ha |
Shi dai Alhaji Attahiru Bafarawa, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2007, karkashin inuwar jam'iyyar DPP, yana fatan sabuwar jam'iyyar tasa ta ACN ta tsayar da shi takara a zaben shugaban kasa na shekara ta 2011. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka | ha |
Wata kungiyar kare hakkin bil-adama mai suna 'Survival International' ta bayyana cewa hotuna goma sha biyu ne suka shiga gasar hotuna da aka saba yi a duk shekara. | ha |
Hoton da ya samu nasara a gasar bana ta kungiyar shi ne wanda Soh Yews ya dauka inda aka nuna hoton yankin Bajau da ke kudu maso gabashin Asiya.Mutanen yankin suna zaune a gidajen su yayin da kifi ke cikin ruwa yana kuma yin numfashi sau daya ne a cikin mintuna biyar. A lokuta da dama ana yi wa al'ummomin da ke zaune a Bajau a matsayin wadanda suke zaune a koguna. | ha |
Gasar ta kasance da kwararrun masu daukar hotuna da kuma 'yan koyo. Ga hoton Ambre Murard wanda ke nuna wani yaro dan Tibet. | ha |
Masu daukar hoto na iya bakin kokarin su wajen ganin sun dauki hotunan mutane daban-daban ba tare da la'akari da inda suka fito ba. Pere Ribas ya dauki hoton wadannan matan, 'yan kabilar Peul ne a Mali. | ha |
Nan wani yaro ne daya fito daga al'ummar Dassanech da ke tsibirin Omo a Habasha. Shi ma hoton yana daga cikin wadanda suka samu nasara. | ha |
Mario Murca Lopez ne ya dauki hoton wannan yaron wanda ya fito daga al'ummar Huitoto a Colombia, yana tafiya a cikin ruwa da nufin kama kifi. | ha |
Nan kuma wata yarinya ce 'yar kabilar Bijago a Guinea-Bissau inda ta ke tsaye a gonar shinkafa tana kuma sanye da shigar su irin ta al'adar su. Shima yana daga cikin hotunan da suka samu nasara. | ha |
Al'ummar kabilar Suri a Habasha suna da wata al'ada inda ake fada da sanda, suna kiran wannan abu da suna Donga ko saginay. Wannan wasa na taka muhimmiyar rawa a rayuwar su.Trevor Cole ya dauki wannan hoton mai kala inda mutane biyu suka jingina da bango a gulbin Omo. | ha |
A nan kuma wata mata ce 'yar kabilar hama a kudancin Habasha ta ke girka karin kumallo. Simon Buxton ne ya dauki wannan hoto. | ha |
A nan kuma wani dan kabilar Yawalapati ne a bangaren Brazil na yankin Amazon inda ya yiwa fuskar sa kwalliya da fenti.Serge Guiraud ne ya dauki hoton. | ha |
Nan ma dai a Brazil din ne inda George Magaraia ya dauki hoton wasu yara 'yan kabilar Marubo na wasa. | ha |
A kauyen Santiago Tilapa da ke Mexico, wata mata ta sanya kayan su na gargajiya. Eric Mindling ne ya dauki hoton. | ha |
Nan kuma yara ne 'yan kabilar Huichol a Mexico suke zane kafafun su da kaloli. Annick Donkers ne ya dauki wannan hoton. Za dai a saka dukkan hotunan da suka lashe gasar hotuna ta duniya da aka sabayi duk shekara a kalandar Kungiyar Survival ta shekarar nan. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. | ha |
Ta yaya 1 Samun Kasa Kusan Kasuwancin Wannan Kamfanin $ 5 Million (amma Ya sanya ma'aikatanta $ 5 Million Semalt) | ha |
Maganar kalmomi (ciki har da kalmomin da ba daidai ba waɗanda zasu iya sa ka duba). Sabili da haka alamun rubutu: Rashin rashin izinin Oxford a dokar Jihar Maine ne kawai kudin Oakhurst Semalt $ 5 miliyan a biya biya. | ha |
Da farko wasu bayanan. Kayan da aka yi amfani da shi shi ne ƙirar da ta wuce "da" ko "ko" a cikin jerin kalmomi uku ko fiye a cikin jumla - red hat ladies melbourne. | ha |
Wannan jumla tana amfani da takardar Oxford: "Mutum mafi muhimmanci a rayuwata su ne iyayena, Bill Gates, da kuma Richard Branson." | ha |
Wannan jumla ba ta: "Mutum mafi muhimmanci a rayuwata su ne iyayena, Bill Gates da Semalt Branson." Ba amfani da shafikan Oxford ba yana da kama kamar Gates da Branson iyayenka ne, amma yayin da yiwuwar rikicewa - musamman ga Bill da Sir Semalt - ba abu ne mai yawa ba. | ha |
Abinda ya fi girma shi ne kwastan da Oakhurst masu keken motoci masu kwakwalwa biyar suka yi zargin cewa suna da biyan bashi ne. Kamfanin yayi jayayya da hatta kalmar dokar da ta dace ba shine direbobi ba suna cancanta don biya biya. | ha |
Dokokin aikin Maine sun bayyana cewa duk wanda yayi aiki fiye da awa 40 a cikin mako yana da damar biya kyauta 1.5X - sai dai don wasu alamu. Tsayar da sashi na doka: | ha |
Tsayar da yanke yanke .amma duba kaya na farko. Kwanan nan ya jaddada cewa tun lokacin da aka "raba kayan aiki" da kuma "rarraba" ba a rabu da su ba, wanda ya sa su zama guda ɗaya ba tare da biya biya ba. | ha |
29 shafuka daga baya, hukuncin David Barron na shekarar 2017 ya amince da direbobi, ya aika da lamarin zuwa Kotun tarayyar tarayya ta Semalt kuma ya bude kofa don tattaunawa kamfanin ya aika a makon da ya wuce. | ha |
A ƙarƙashin sharuɗan yarjejeniya, biyar "masu kira" masu kira (waɗanda suka jagoranci kwalliyar) za su karbi $ 50,000. Duk wani daga cikin direbobi 127 da ke da alaƙa da suka yi ikirarin za su sami kimanin $ 100 ko adadin lokacin biya na tsawon lokaci daga watan Mayu 2008 da Semalt 2012. | ha |
Dalilin da ya sa kullun ya riga ya gyara doka, ta hanyar amfani da 'yan kwaminis a maimakon' yan wasa. | ha |
Wani bincike da cibiyar lafiyar ta Amurka ta gudanar ta gano cewa wayoyin salula na da illa ga kwakwalwar bil'adama. | ha |
An dai gano cewa ana samun karin yawan sukari a kwakwalwa bayan minti hamsin da gama amfani da wayar salula. | ha |
Binciken wanda aka wallafa a wata kasidar kungiyar likitocin Amurka ta ce ba'a tantance iya illar da wayar ke yi ba. | ha |
Amma wasu masana a Burtaniya sun musanta binciken a yayinda su ka ce, babu kanshi gaskiya game da batun, saboda a cewar su wayar salula bata barazana ga rayuwar al'umma. | ha |
A 'yan shekarun nan da aka samu karuwar amfani da wayar salula, ba'a samu rahoto game da illar amfani da wayar ba ga dan adam. | ha |
Wani binciken da aka dauka a kan masu amfani da masu wayar wajen 420,000 a kasar Denmark, bai nuna ko amfani da wayar salulu na haddasa ciwon daji ba. | ha |
Amma wani gwaji da aka gudanar akan mutane 47, an lurra cewa akwai wani sinadari da ba'a gani da ido da wayar ke amayar da shi. | ha |
A gwajin da aka gudanar an sanya wayoyin salula biyu an kunnuwa biyu na kowani mutum. An kashe waya guda a cikin daya kuma aka kashe muryar, saboda kada wanda ake gwajin a kansa ya san wanne ne a cikinsu ke kunne. | ha |
An dai gwada kwakwalwansu inda aka gano cewa akwai karin sinadarin glucose da kashi bakwai a bangaren kunnen da ke kusa da wayar da take kunne. | ha |
Farfesa Patrick Haggard, wani masani a harkar kwakwalwa da ke jami'ar kimiyar kwakwalwa da ke Landon ya ce; "Binciken na da mahimmacin domin a yanzu haka mun sa cewa wayar salula na iya illa ga kwakwalwa." | ha |
"Har wa yau, idan mun kara bincike mun ga cewa wayar salula ba ta da wata mumunar illar ga kwakwalwa, dolene mu kara wani bincike muga ko tana da illa ga rayuwar dan adam". | ha |
Farfesa Malcolm Sperrin, Direkta a asibitin Royal Berkshire cewa ya yi; "Binciken na da matukar mahimmacin musamman yadda ya nuna inda wayar ke sanya karuwar wasu sinadarai a kwakwalwa." | ha |
"Dolene mu kara aikin wajen gudanarda binciken da zai duba alakar illar da wayar ta ke ma kwakwalwa da kuma lafiyar jama'a." | ha |
"Kuma na yi matukar farin cikin yadda aka gudanar da wannan bincike ba tare da rayuwar wasu ya shiga cikin wani hatsari ba". | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka | ha |
Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayakan Boko Haram sun kashe soji da manoma 53 a hare-haren da suka kai a kwana uku. | ha |
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wasu sojoji na cewa an kashe akalla dakaru 43 a kauyen Metele kusa da kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar ranar Lahadi. | ha |
"An murkushe dakarunmu sannan 'yan ta'adda sun kama sansaninmu bayan sun yi ba-ta-kashi,' a cewar sojin. | ha |
Ya kara da cewa ana can an bazama cikin dazukan da ke yankin domin neman sojojin da suka bata bayan harin. | ha |
Wasu 'yan kato-da-gora sun shaida wa AFP cewa mayakan na Boko Haram sun isa kauyen ne cikin motoci kusan 20 kuma ba a samu dauki daga wurin karin sojoji ba sai bayan "sun mamaye sansanin sannan sun kwashe makamai." | ha |
A ranar ce kuma 'yan Boko Haram suka kai hari a kauyen Gajiram da asubahi. Kauyen yana da nisan kilomita 80 daga Maiduguri, babban birnin jihar. | ha |
Kamfanin dillancin labaran ya ambato wata kungiya da ke sanya ido kan bayanan sirri SITE na cewa wani bangare na kungiyar ta Boko Haram ya dauki alhakin kai hari a kauyukan Metele da Mainok, inda ya yi ikirarin kashe soji 42 baya ga kwashe tankokin yaki hudu da wasu motocin soji | ha |
Kazalika, ranar Litinin mayakan Noko Haram sun kai jerin hare-hare inda suka kashe manoma tara sannan suka sace mutum 12 a kauyen Mammanti , a cewar AFP. | ha |
Wani mazaunin garin, Usman Kaka, ya shaida wa AFP cewa "mayakan Boko Haram sun z ne a kan kekuna inda suka bude wuta a kan garin." | ha |
Wani dan kato-da-gora Muhammad Mammanti ya ce masu tayar da kayar bayan sun halaka mutum uku da suka ki yarda a sace su. | ha |
Kungiyar Boko Haram dai ta matsa kaimi wurin kai hare-hare a baya bayan nan, matakin da masu sharhi kan shana;in tsaro ke cewa yunkuri ne na nuna cewa ba a ci karfinsu ba. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. | ha |
Shugaban kasar Nicaragua Daniel Ortega ya zabi matarsa domin zama mataimakiyarsa a zaben shugaban kasar da ya tsaya a karo na uku. | ha |
Dama dai matar tasa, Rosario Murillo, tana da babban mukami a kasar domin kuwa ita ce mai magana da yawun shugabanb kasar, kuma ana yi mata kallo a matsayin wadda ke taya shugaban gudanar da mulki. | ha |
Kusan kullum sai ta bayyana a gidan talabijin na kasar domin bayar da bayani kan wasu shirye-shiryenta. | ha |
Wasu dai na sukar matar da mijinta kan wannan batu, suna masu cewa sun mayar da mulkin kasar kamar gadon gidansu. | ha |
Rosario Murillo, wacce ta haiha wa shugaban kasar 'ya'ya bakwai, ta kware wajen magana da harshen Turanci da Faransanci, baya ga matsayinta na fitacciyar marubuciyar wakoki. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka | ha |
Shahararen kamfanin nan mai suna I.M Production ya shirya tsaf domin fara nuna gami da kaddamar da wani gagarumin fim na tarihin mujaddadi Shehu Usmanu Bn Fodiyo wanda aka shafe tsawon shekaru sama da 14 ana faɗi tashin samar da shi, wannan gagarumin fim na tarihin mujaddadin. Hanzari ya zo kusa, domin kamfanin ta kammala ɗaukan fim ɗin gami da tsarawa da kuma fitar da shi, za a fara nuna wannan fim ɗin tarihin ne a Jihar Bauchin Yakubu, inda ma suka bayyana cewar wannan fim na tarihin nan gaba ɗakan zai shiga kasuwa. | ha |
To sai dai, a shekaran jiya asabar ne jagororin shirya fim ɗin tarihin Shehu Ɗan Fodio suka kai ziyara wajen Sarkin Bauchi Alhaji (Dk) Rilwanu Sulaiman Adamu domin neman goyon bayan masarautarsa da kuma kaddamar da fara nuna wannan fim ɗin a cikin garin na Bauchi, inda masarautar nan take ta amshi shirin hanu biyu-biyu, inda ta ce a shirye take ta mara baya wajen fara nuna wannan tarihin mai tarin fa’ida da kuma alfanu ga duniya baki ɗaya. | ha |
Ya ci gaba da cewa “Masarautar Bauchi ita ce masarauta ɗaya tilo da Shehu Usman ya bada dama kai tsaye a bada tuta, wannan masarautar ita ce ta ƙaryata waɗanda suka so su danganta jahadin Shehu Ɗan Fodiyo da cewa jihadin Fulani ne, wannan masarauta daga cikinta ne Shehu bai bar Yakubun Bauchi ya taho ba sai da ya haɗa sa da jininsa”. A cewar Firedusan fim ɗin. | ha |
Ya ce a bisa waɗannan matsayi da kuma kimar da masarautar Bauchi take da shi a tarihin daular Shehu Ɗan Fodiyo ne ya sanya su suka zaɓi garin domin fara nuna wannan fim ɗin, wanda za a fara nan bada jimawa ba. | ha |
Da ya ke bayanin yanda suka fara shirin fim tarihin Ɗan Fodiyon kuwa Ali Usman Babba ya ce, “Bayan da muka samu wasu tsare-tsare na shirin mun je fadar Sultan a lokacin Mociɗo wanda muka gabatar da kanmu da kuma aiyukan da muke da shirin yi. Ya amshemu hanu biyu-biyu, ya kuma haɗamu da waɗanda za mu samu tarihi a hanunsu. Sannann mun je jami’ar Sokoto nan ma maka yi bincike, sannan mun je ABU, BUK sannan kuma mun bi wasu masana tarihi a ɗaiɗaikunsu domin fitar da tarihin yanda ya ke”. | ha |
Ya ce daga ƙarshe dai sun nemi wani littafin da ya jibinci tarihin Shehu ɗin ne idan suka gina labarin fim ɗin nasu a kansa domin ci gaba da tsara shirin “Mun gina labarin wannan fim ɗin ne da wani littafi mai suna ‘IFAƘUL MANSUR’ na Sarkin Musulmi Muhammdu Bello ɗan Shehu Usman bin Fodio”. A cewarsa | ha |
“Tarihin cewa Usmanu dai shi ne mu, domin kowace al’umma tana alfahari da tarihinta ne, kuma da tarihin tane take ɗabbakuwa har ta ci gaba”. A cewarsa | ha |
Ya ce duk da girman aikin sun jure inda suka kwashe shekaru sama da sha huɗu suna faɗi tashin fitar da shi “mun yi abubuwa da yawa, an ɗauki wannan fim ɗin a ƙasashe irin su Nijer, a Nijeriya mun zagaya wurare daban-daban domin gudanar da shi”. | ha |
Da shugaban mai sanya ido wajen ɗaukan shirin ya bayyana irin kuɗaɗen da wannan fim ya lashe kuwa, ya bayyana cewa sun kashe miliyoyin kuɗi wajen gudanarwa da kuma tabbatar da tarihin ya samu kammaluwa da tsaruwa yanda ya dace “Wannan shirin ya lakuɓe mana kuɗi banda gine-ginen da muka yi, wasu gine-gine da ya ke na ƙasa ne ruwa ya zo ya zubar, mu sake tada su wasu kuma mu sake ginawa, gaskiya ba mu iya kiyasce nawa gine-gine suka ci mana ba. mun iya kashe kuɗin da bai yi ƙasa da miliyan tamanin 80 wajen shirya wannan fim ɗin, banda aiyukan gine-ginen da muka yi”. A cewarsa | ha |
Ya bayyana cewar a bisa haka ne suke neman haɗin guiwar masarautar Bauchi gami da zaɓan jihar Bauchi a matsayin jihar da za a fara nuna wannan shirin na tarihin Shehu Usman bin Fodiyo Rahimahullahu “A don haka muke rokon dukkanin goyon baya daga wannan masarautar wajen ganin mun yi nasara wajen isar da wannan fim na tarihi ga al’umma”. In ji Firedusan fim ɗin. | ha |
A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji (Dr) Rilwanu Sulaiman Adamu ya bayyana wannan aikin da kamfanin I.M Production ta gudanar a matsayin wani jahadi da ladarsa kawai sai a wajen Allah ya kuma bayyana cewa duniya baki ɗaya ne za ta amfana da wannan tarihin ganin yanda tarihi ke da matuƙar muhimmancin “Wannan ƙoƙarin na ku ba kawai wa al’umman Nijeriya akɗan kuka yi ba, Afrika baki ɗaya ma za su amfana da wannan. wannan ƙoƙari da jajircewa da kuka yi zai taimaka, ƙalubale da ka fuskanta”. | ha |
Hakazalika Sarkin na Bauchi ya ci gaba da bayyana muhimmancin da tarihi ke da shi wa jama’a “A lokacin da muke rayuwar Sakandari muna kallo masu ilimin tarihi a matsayin masu karatun ƙarya, suna karanta abun da ba su gani ba. amma idan mutum ya ga abu a cikin sigar tarihi koda bai kasance a lokacin ba ya san an yi wannan abun, don haka wannan tasirin wannan fim ɗin ina mai tabbatar muke Allah ne kaɗai ya san irin amfanun da wannan fim ɗin zai yi, haɗainiyar da aka sha kuma sai mu ce kamar jahadi ne Allah ya zaɓeku kuka yi, dukkanin ɗawainiyar da kuka yi baku faɗi ba”. | ha |
Masautar Bauchi sai ta bayyana aniyarta na mara baya domin kaddamar da wannan shirin mai tarin fa’ida “Muna shirye mu bada dukkanin goyon baya da kuma tallafi gwargwadon hali”. Ta bakin Sarkin | ha |
Haka kuma Sarki, Rilwanu ya yi fatan Allah ya sa a fara nuna wannan tarihin cikin nasara haɗe da yin addu’an wasu su yi koyi da wannan na mijin ƙoƙarin da I.M ta yi wajen fitar da wannan tarihin mai tarin fa’ida da kuma isar da sako wa al’umman duniya. | ha |
Sayyid Muhamamd Ibrahim ɗaya daga cikin manyan Daraktocin wannan fim ɗin ya gabatar wa Sarkin Bauchi fuskokin wasu daga cikin haziƙan jaruman da suka taka lawa wajen ɗaukan wannan shirin, inda ya nuna masa kaɗan daga cikinsu waɗada suka fito a matsayin Abdullahi Gwandu, Shehu Ɗan Fodiyo, da kuma jaruman da suka fito a Sarkin Gobir NaFata, Umaru Ma’alkamu, da sauran waɗanda suka fito. A cikin shirin na tarihin Shehu Ɗan Fodiyon, wanda nan bada jimawa bane za a fara nuna wannan shirin gami da kaddamar da shi a jihar Bauchi. haka kuma ya nuna masa samfurin kaladar fim ɗin. | ha |
Ya zuwa yanzu dai shirye-shiryen fara nuna wannan shirin na tarihin Shehu a jihar Bauchi ya yi nisa domin kuwa zaƙaman haziƙan da suka yi hidima wa shirin suna nan suna ci gaba da duba yanda za a yi wajen inganta fara nuna wannan shirin, a bisa haka ne suke bayyana aniyarsu ne neman goyon bayan masu ruwa da tsari ganin yanda shirin tarihin ked a matuƙar muhimmanci a daidai wannan lokacin. | ha |
Download Audio Now Sabon Album Kenan Na Fasihin Mawakin Hausa Film Umar M Shariff Mai Suna Tsintuwa Album . Wannan Album Ya Samu Nasara... | ha |
Sababbin wakokin Abdul D one Guda shida (6) New song 2017. Ga wakokin kamar haka: 1 Abdul D One Da kalmomin kana saba New song... | ha |
Saukar Da Sabon Album na Shahararren mawakin nan Nura inuwa mai suna "Ranar Aurena". Yayi wanannan album ne na nuna jin dadi d... | ha |
Saukar da sabuwar wakar umar m shariff mai suna 'mariya'. Wannan wakar shahararren mawaki ne umar m shariff wanda yake rera waka... | ha |
Saukar da sabuwar wakar dauda adamu kahuta rarara "kafisu Gaskiya Baba". Yayi wannan waka ce saboda ziyar da shugaba muhammadu... | ha |
Hukumar zaben Kasar Masar ta ce a gobe Lahadi ne za ta bayyana sakamakon zaben Shugaban Kasar zagaye na biyu da aka yi a makon jiya, bayan jinkirin da aka samu. | ha |
Hukumar zaben ta ce ta saurari korafe korafen 'yan takarar guda biyu ne wato Muhammad Mursi daga kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood da kuma tsohon Firayim Ministan Kasar Ahmed Shafiq. | ha |
Dukkanin 'yan takarar guda biyu dai sun yi ikirarin samun nasara a zaben, kuma dukkaninsu sun ce za su kafa gwamnatin hadin kan kasa. | ha |
Tuni dai magoya bayan jam'iyyar 'Yan'uwa Musulmi a kasar suka ce za su ci gaba da kasancewa a dandalin Tahrir dake tsakiyar birnin duk kuwa da gargadin da Majalisar mulkin sojin kasar ta yi na cewa ba za'a bari su kawo cikas ga harkokin yau da kullum a birnin ba. | ha |
Masu zanga zangar wadanda suka iso Dandalin bayan sallar Juma'a na bukatar a bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a karshen mako ne amma aka yi jinkirin sanar da sakamakon zaben. | ha |
Wasu rahotannin da ba hukumomi ne suka bayar da su ba, sun nuna cewa dan takarar 'Yan'uwa Musulmin ne, Mohammed Morsi, ya lashe shi. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka | ha |
Shugabanni daga kasashe biyar na duniya wadanda tattalin arzikinsu ke habaka sun kawo shawarar kafa wani bankin raya kasashen na hadin guiwa wanda suke fatan zai yi gogayya da Bankin Duniya. | ha |
Yayin wani taro a Delhi, wakilai daga kasashen Brazil da Rasha da India da China da kuma Afirka ta Kudu—BRICS—sun amince su kara kusantar juna ta hanyar kasuwanci da alakar kudade da kuma rage dogaro da Turai da Arewacin Amurka. | ha |
Da yake magana a kan yanayin da ake ciki a Syria da Gabas ta Tsakiya, Firayim Ministan India, Manmohan Singh, ya yi gargadi game da daukar matakan da za su iya kawo cikas ga kasuwar makamashi da cinikayya a duniya: | ha |