text
stringlengths 101
6.99k
| language
stringclasses 1
value |
---|---|
An zargi wata mace 'yar ƙasar Italiya da ƙaryar samun juna biyu, kuma ta je ta mayar da jaririyar da ta sayo, bayan ta gano cewa yarinyar ruwa biyu ne. | ha |
An zargi matar 'yar shekara 35 da sayen jaririya a kan kuɗi dala 21, 800 kwatankwacin naira miliyan bakwai. | ha |
An kama matar tare da mahaifiyar jarirai ta ainihi da kuma wani ɗan ƙasar Morocco da ake zargin shi ya haɗa cinikin. | ha |
Al'adar ba da goyon ciki haramun ne a ƙasar Italiya, inda akan yi mutum ɗauri a gidan yari da cin tara mai tsanani. | ha |
An ce uwar bogen ta faɗa wa 'yan sanda cewa ta riƙa kifa wani cikin ƙarya da ta saya ta hanyar intanet don yaudarar dangi da ƙawayenta. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. | ha |
Arsenal ta kawar da matsalolin da take fama da su a kwanakin nan gefe daya ta yi abin a-zo-a-gani wajen doke masu masaukinta AC Milan 2-0, wasan farko na matakin kungiyoyi 16, na kofin Europa. | ha |
Gunners din sun je wasan ne a yanayi na koma baya da ba su taba shiga ba a tsawon shekara 22 na jagorancin kociyansu Arsene Wenger, da kuma rashin nasara sau hudu a jere da ake doke su. | ha |
Bal din farko ta Henrikh Mkhitaryan a kungiyar ita ce ta sa su gaba a minti na 15 da shiga fili, sai kuma ta biyu wadda Aaron Ramsey ya ci dab da tafiya hutun rabin lokaci. | ha |
Da kwallo biyun da Arsenal ta ci yanzu a gidan AC Milan ana ganin tana kusa da samun damar zuwa wasan dab da na kusa da karshe na gasar ta Europa, idan har ta kara yin galaba a karawarsu ta biyu ranar Alhamis mai zuwa a filin Emirates. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka | ha |
Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce dirar mikiya da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya-DSS a kasar ke yi kan manyan alkalan kasar, an dauko hanyar kashe dimukradiyyar kasar ce. | ha |
Cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaranta na kasa, Prince Dayo Adeyeye ya fitar, jam'iyyar ta yi zargin cewa dirar mikiyar, ta kara fito wa fili da salon kama-karya da gwamnatin Muhammadu Buhari ke yi. | ha |
Jam'iyyar ta ce a halin yanzu, alkalai hudu ne, da suka hada da Sylvanus Ngwuta da Inyang Okoro na kotun koli, da kuma Muazu Pindiga da Adeniyi Ademolada na manyan kotu na ke tsare a hannun hukumar ta DSS. | ha |
Jam'iyyar ta PDP ta ce da badan jajircewar da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya yi ba, da jami'an hukumar ta DSS sun kama alkali na biyar, Mai shara'a Abdullahi Liman. | ha |
A cikin sanarwar, jam'iyyar ta PDP ta yi zargin cewa lokacin samamen, jami'an hukumar ta DSS sun ci zarafin alkalan, sannan suka lakadawa wasu ma'aikatan gidajensu duka. | ha |
Ta kuma bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na shugaba Muhammadu Buhari na mayar da bangaren shari'a 'dan amshin Shata'. | ha |
Ta ce kamata yayi a bi hanyoyin da ya kamata idan ana zargin alkalan da aikata laifi, ta hanyar aikewa ta takardun koke ga hukumar dake kula da ayyukan alkalai ta kasa. | ha |
Jam'iyyar PDP ta kuma bayyana wasu abubuwa da ta ce yi wa dokar Najeriya karan tsaye ne da gwamnatin Muhammadu Buhari ke yi, wadanda suka hada da yin dirar mikiya da jami'an DSS suka yi a majalisun dokokin jihohin Akwa Ibom da Zamfara, da ci gaba da tsare mutane da dama duk da umurnin sakinsu da kotu ta bayar. | ha |
"Ko a lokacin mukin kama-karya na Sani Abacha ba ayi wa ma'aikatan bangaren shari'a irin wannan dirar mikiya ba" PDP ta ce. | ha |
"Shugaba Buhari ya nuna ba ya mutunta turakun demukradiyar kasar nan. Ya nuna ya na so ya kashe dimukradiyyar, ya mayar da ita mulkin kama-karya", jam'iyyar ta kara da cewa. | ha |
Jam'iyyar ta ce gwamnatin Najeriyar ta ki ta mutunta umurnin kotun ECOWAS game da Kanar Sambo Dssuki. | ha |
Jami'an hukumar sun kaddamar da sumamen ne a babban birnin kasar, Abuja da Port Harcourt da Gombe da Kano da Enugu da kuma Sokoto. | ha |
Ko makonni kimanin biyu da suka gabata sai da Hukumar da ke sa ido kan harkokin shari'a a kasar ta kori wasu manyan alkalai bisa samun su da laifin cin hanci. | ha |
An dai kori babban alkakin kotun jihar Kano, mai shari'a Kabiru Auta da babban alkalin kotun daukaka kara da ke zama a Ilorin, mai shari'a Mohammed Ladan Tsamiya. | ha |
Hukumar ta ce ta kori wasu daga cikin alkalan bisa karbar na-goro game da batutuwan da suka shafi zaben kasar na shekarar 2015. | ha |
Tun dai hawan mulkin kasar, Muhammadu Buhari, ya lashi takobin yaki da rashawa da cin hanci da suka yi wa kasar dabaibayi. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. | ha |
Majan kulob din Manchester United Sir Alex Ferguson ya soki rafali Lee Mason saboda rashin soke cin da kulob din Birmingham suka yi wa kulob dinsa a 'yan mintunan karshe na wasan da suka tashi daya da daya. | ha |
Ferguson ya ce kwallon ta taba hannun dan wasan Birmingham kuma an yi wa Rio Ferdinand keta kafin a ci kwallon, amma rafali ya kau da kai. | ha |
" Shi ya sa muka ce wa hukumomin gasar Premier su nemo rafali da zai iya ganin irin wadannan laifuka da 'yan wasa suke aikata wa a filin wasa." In ji Ferguson. | ha |
Kulob din na Manchester dai da farko yana gaban Birmingham da da ci dayan da Dmitar berbatov ya jefa masa, kafin daga bisani ana sauran 'yan mintuna a kare wasan Lee Bowyer na kulob din Birmingham ya farke. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. | ha |
Majalisar Dattawan Najeriya ta ki tabbatar da sunayen wadanda shugaban kasar, Muhammadu Buhari, ya nada a matsayin kwamishinonin hukumar zaben kasar INEC. | ha |
Majalisar ta yi hakan ne a wani mataki na ramako ga bangaren zartarwar kasar kan ci gaban mukadashin shugaban hukumar yaki da cin hanci ta EFCC da zama a kan kujerarsa bayan 'yan majalisar sun ki tabbatar da shi. | ha |
Zaman majalisar na ranar Talata, wanda shugabanta Bukola Saraki ya jagoranta, ya dakatar da nazari kan sunayen kwamishinonin INEC 27 din da Buhari ya tura majalisar ne har sai bayan mako biyu. | ha |
Daga farko dai 'yan majalisar sun nemi hana majalisar magana kan tantance sunayen kwamishinonin ne gaba daya, amman daga baya Sanata Saraki da mataimakinsa Ike Ekwerenmadu, sun nemi 'yan majalisar su yi hakuri a dakatar da tantancewar na wucin gadi. | ha |
Bayan haka ne Sanatan da ya gabatar da kudirin dakatar da tantancewar, Sanata Peter Nwaboshi da ke wakiltar Delta ta Arewa, ya gyara kudirin nasa, kuma majalisar ta amince da hakan. | ha |
Wasu daga cikin 'yan majalisar sun yi ikirarin cewar mukadashin shugaban hukumar EFCC yana musu bita-da-kulli bayan sun ki tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar. | ha |
A ranar Ltinin ne dai kafafan yada labaran kasar suka byar da rahoton cewar Ibrahim Magu ya mika wa shugaban kasar, Muhammadu Buhari, wani rahoton da ke cewa shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki, ya wawushe naira biliyan 3.5 a cikin kudin lamunin Paris Club din da aka mayarwa Najeriya. | ha |
Amman Saraki ya musanta hakan yana mai cewar ramakon gayyan ne mukaddashin shugaban EFCC ke yi don kin tabbatar da shi a kan mukaminsa. | ha |
Rahotanni dai sun ce an mika wa Shugaba Buhari rahoton na EFCC ne ranar 10 ga watan Maris inda Majalisar Dattawan kasar ta ki tabbatar da Ibrahim Magu a mukaminsa ranar 15 ga watan na Maris. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. | ha |
Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta tabbatar da karbar 'yan gudun hijira kimanin 300 wadanda rikicin Boko Haram ya tilastawa ketarawa zuwa kasar Chadi. | ha |
Rahotanni dai na cewa kasar ta Chadi ta mayar da 'yan Najeriyar masu neman mafaka a yankinta ne saboda yawan da suka yi mata. | ha |
Alhaji Mohammed Kanar, wakilin hukumar ta NEMA mai kula da yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa akasarin mutanen da aka mayar da su 'yan jihar Borno ne kuma dukkannin su suna cikin koshin lafiya. | ha |
Ya kara da cewa hukumar ta nema ta tarbi mutanen a sansaninta kuma za a mayar da su garuruwansu idan har akwai yiwuwar hakan. | ha |
Rahotanni sun ce ko a watan Mayun 2015 ma, Jamhuriyar Nijar -- wadda makwabciyar Najeriyar -- ta mayar da 'yan Najeriya sama da dubu uku masu neman tsira a cikin kasar a wani mataki na hana yaduwar Boko Haram a kasar. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka | ha |
'Yan tawayen na Libya dai sun yi tattaki zuwa Amurka ne domin su yi kokarin ganin sun kara samun goyon baya ta fuskar siyasa da tattalin arziki. | ha |
Sun kuma je kasar ta Amurka ne domin su karbi kadarorin Libya wadanda aka sanyawa tankunkumi da yawansu ya kai biliyoyin daloli. | ha |
Fadar ta White House ta ce bangarorin biyu sun tattauna a kan yadda Amurka da kawancen kasashen duniya za su kara taimaka musu kuma sun sake yin kira ga Shugaba Gaddafi ya sauka daga kan mulki. | ha |
Kakakin gwamnatin Amurka, Mark Toner, ya ce gwamnatin ta Amurka za ta ci gaba da yin nazari a kan Majalisar Rikon Kwarya ta 'yan tawayen, wato Transitional National Council. | ha |
Sai dai ya ce wuka da nama na hannun jama'ar Libya wurin yanke shawara, ba kasashen duniya ba, a kan wanda zai jagoranci kasar nan gaba. | ha |
Amma Mista Toner ya ce Amurka ta dauki 'yan tawayen Majalisar Rikon Kwaryar a matsayin ingantattun, kuma halattattun, wakilan jama'ar Libya. | ha |
Sai dai Amurka da Birtaniya ba su bayyana 'yan tawayen a matsayin halattacciyar gwamnatin Libya ba kamar yadda Faransa, da Italiya, da Qatar suka yi. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka | ha |
Hukumar kwallon kafar Ingila, ta hukunta daraktan wasanni na kulob din QPR, Les Ferdinad saboda samunsa da rashin da'a. | ha |
Haka kuma FA ta ci tarar Ferdinand mai shekaru 48 fam 12,000, ta kuma ce ba zai ziyarci dakin sauya kayan 'yan wasa da hanyar da suke bi su shiga fili ba. | ha |
An samu Ferdinand da laifin ne a karawar da Tottenham ta doke QPR da ci 2-1 a gasar Premier, a inda ya fadawa alkalin wasa bakaken maganganu. | ha |
Hukumar ta ce hukuncin da ta yanke wa Ferdinad wanda ya karbi aiki da QPR a watan Oktoba ya fara aiki nan take. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. | ha |
An kawo karshen harbe-habe da fashewar bama-bamai da suka rika tashi a Jakarta, babban birnin Indonesia. | ha |
Bama baman sun tashi ne a wani rukunin shaguna da ke kusa da fadar shugaban kasa da kuma ofishin Majalisar Dinkin Duniya. | ha |
Da ma dai 'yan sanda sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar kai wa kasar hari, kuma sun yi kira a kara matakan tsaro. | ha |
Shugaban kasar Joko Widodo ya ce ba za su bai wa 'yan ta'addda kai bori ya hau ba, yana mai yin kira ga 'yan kasar da su ci gaba da jajircewa wajen ganin an kawar da 'yan ta'adda. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka | ha |
Da yake magana a Ilorin, jihar Kwara a ranar Talata 17 ga watan Janairu, basaraken ya bayyana cewa ayyukan kungiyar yan ta'addan ba koyarwan ... | ha |