text
stringlengths 101
6.99k
| language
stringclasses 1
value |
---|---|
Jim kadan bayan ya dawo daga New York inda ya je taron Majalisar Dinkin Duniya, Netanyahu tare da wasu manyan jami'an tsaron kasar Israila suka yi wani taron gaggawa dangane da yawan tashin hankali da Falasdinawa ke haddasawa kan Israilawa. | ha |
Firayim Ministan ya ce zasu hanzarta rushe gidajen 'yan ta'ada. Zasu kara yawan jami'an tsaro a birnin Qudus tare da West Bank. Bugu da kari Israila zata daure duk wanda ake kauatata zaton dan ta'ada ne ba tare da bata lokaci ana wata doguwar shari'a ba. | ha |
Tun farko 'yansandan Israila suka sanarda dakatar da Falasdinawa daga shiga tsohon birnin Qudus. Ban da haka duk namiji mai shekaru kasa da 50 ba za'a bari ya shiga Masallacin al-Aqsa ba. | ha |
Masallacin na cikin daya daga wurare masu tsarki ga addinin musulunci kuma nan ne aka fi samun tashin hankali cikin 'yan kwanakin nan. | ha |
Wasu Israilawan da Falasdinawa masu sassaucin ra'ayi sun damu da yawan tashin hankali abun da suka ce wata alama ce dake nuni da barkewar tashin hankalin gama gari nan gaba. | ha |
Taron majalisar ministoci na karshe na jamhuriyar Nijer ya dauki kudurin yin ragowar kudin wutar lantarki ga daukacin ‘yan kasar. | ha |
Wannan labari ya farantawa ‘yan kasar rai ganin cewa biyan kudaden wuta na daya daga cikin abubuwan da ke da wahalar gaske bias la’akari da irin tattalin arzikin kasar. | ha |
A cewar Malam Sufuyanu, wannan shiri da gwamnati ta yi domin taimakawa talakawa abin farin ciki ne kwarai da gaske, domin daya daga cikin matsalolin da ke addabar talakawa da ya kamata gwamnati ta duba itace tsadar wutar lantarki. | ha |
Wannan mataki da gwamnatin Nijer ta dauka zai fara aiki ne daga farkon watan Janairun shekara mai zuwa, hakazalika sanarwar ta tayi Karin bayanin cewa wannan atakin zai ba masu karamin karamin karfi damar cin gajiyar wutar lantarki yayin da nauyin biyan kudin wutar zai koma hannun manyan kamfanoni. | ha |
‘Yan kasar da dama sun bayyana ra’ayoyinsu musamman ganin yadda lamarin ya dade yana ci masu tuwo a kwarya koda shike wasu sun ce ai sun gani a kasa. | ha |
Shugaban kasar Koriya ta kudu, Roh Moo-Hyun ya bayyana fatan ci gaba da tattauna batun makaman nukiliyar Koriya ta arewa tsakanin kasashe shida wanda zai kawo karshen matsalar batun makaman. A sakon sabuwar shekara da kuma taro da ‘yan jaridu a fadar gwamnati a Seoul Mista Roh ya ce yanzu akwai yanayin da ya dace na ci gaba da tattuna batun bayan dakatar da shi da aka yi. Ya kuma ce ba zai iya fadar takamaimiyar ranar ci gaba da tattaunawar ba amma ya ce yana fatan za a ci gaba da tattaunawar da zaran an rantsar da shugaba Bush domin yin wa’adi na biyu a kan mulki. | ha |
Koriya ta arewa ta kauracewa tattaunawar a watan Satumba bayan da kasar Sin ta dauki bakwancin taron da bai samu nasara ba har sau uku wanda ya hada da Japan da Rasha da kuma Amurka . Koriya ta arewa ta ce tana son gwamnatin shugaba Bush ta sauya yanayinta wanda ta kira na ‘’rashin ya kamata’’ da babban agaji. | ha |
Amurka na bukatar Koriya ta arewa ta nunawa duniya cewa a zahiri ta jingine shirinta na kera makaman nukiliya kamar yadda ta yi alkawura karkashin yarjejeniyoyin kasa-da-da-kasa. Shugaba Roh ya lasufta irin matsalar da za a iya samu ta dangantaka tsakanin kasashen biyu amma yace a shirye ya ke da duk wani taro amma y ace da alama shugaba Kim Jong 11 ba zai yadda da wata rana a kusa ba. | ha |
Kasashen biyu sun rabu shekaru sama da hamsin da suka wuce kuma ba su taba sanya hannu kan wata yarjejeniya ba tun karshen yakinsu na shekarar alif da dari tara da hamsin da uku. A wani batu kuma Mista Roh ya ce dakarun Koriya ta kudu za su ci gaba da kasancewa a cikin shirin samar da zaman lafiya a Iraqi ko da bayan zaben kasar na karshen wannan watan. Ya ce dakarun za su ci gaba da aiki har sai an samu zaman lafiya a Iraqi. Amma ya ce ba ya zaton zamansu zai dauki wani lokaci mai tsawo. | ha |
Biyo bayan bada sanarwar ganin watan Ramadan da Mai Martaba Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III yayi jiya Lahadi, malaman Islama sun kira a dage wajen addu'a don samun sauki yayinda yau Musulmi suka tashi da azumi a duk fadin Najeriya da ma duniya gaba daya | ha |
To saidai shigowar watan Ramadan na bana ya zo ne lokacin da darajar Nera ta fadi a kasuwar canji da kuma faduwar farashin gangar man fetur a kasuwar duniya da hakan ya sanya raguwar samun kudi, lamarin da ya sa har jihohi ishirin da bakwai basa iya biyan albashi. | ha |
Ganin halin da kasar ke ciki, malaman Islama sun kira al'ummar Musulmi su dage wajen yin addu'a lokacin wanna watan Ramadan don samun sauki. | ha |
Malamin Ahalu Sunna, wato IZALA, Imam Abdulahi Bala Lau, yace lokutan da suke salla su dinga addu'a Allah Ya yi jagora ga shugabannin kasar a kuma zauna lafiya a Najeriya. Ya kira 'yan kasuwa su sassauta farashinsu, kada su kula da ribar da zasu ci domin su taimakawa jama'ar Allah. Yace hatta wanda ba musulmi ba ya ga an samu sassaucin farashin kaya a wannan wata mai albarka. | ha |
Su ma dattawan arewa da suka hada da Justice Mamman Nasir na kira a yiwa kasar addu'a. Yace ba za'a yi abun kirki ba sai sun nemi zaman lafiya da yadda shugabanni zasu taimakesu. Yace su yi iyakar kokarinsu su zauna lafiya. Ya kira jama'a kada su yi fada amma su cigaba da addu'a. Ya roki Allah Ya Karawa shugabannin Najeriya basira ta yadda zasu taimaki al'ummar kasar. | ha |
Shi ma Shaikh Yakubu Musa Hassan Katsina yace a duk masallatai a dinga sanya gwamnatin Buhari cikin addu'a, musamman ma shi shugaban kasa Muhammad Buhari Allah Ya kara masa lafiya, ya bashi fasaha, ya yi mishi jagora. A yiwa shugaban kasa addu'a Allah Ya azurtashi da mashawarta na kwarai. Ya yi fatan wadanda suke yiwa gwamnatin Buhari zagwon kasa Allah Ya tona masu asiri. | ha |
Haka nan kwamishanan bincike da labaru na hukumar alhazai wanda ya ajiye aiki kwanan nan Dr.Sale Okenwa ya bayyana mahimmancin watan Ramadana ga Musulmi. Yace lokacin azumi lokaci ne da mutum ya kamata ya yi nazari akan rayuwarsa. | ha |
Kungiyar tarayyar Kasashen Afirka, da Tarayyar Turai da Amurka, da Faransa da wasu kasashen sun ce Alassane Ouattara ne suka amince da shi a zaman zababben shugaban kasa | ha |
Dukkan ‘yan takara biyu a zaben shugaban kasa na Ivory Coast ko Cote D’Ivoire, sun yi rantsuwar fara aiki jiya asabar a yayin da kasar ta abka cikin rikicin siyasa. | ha |
An rantsar da shugaba Laurent Gbagbo a wani bukin da gidan telebijin na kasar ya nuna, a bayan da Majalisar Tsarin Mulkin Ivory Coast ta ce shi ne ya lashe zaben da kashi 51 cikin 100. Amma tun farko, hukumar zabe ta kasar ta ce shugaban hamayya Alassane Ouattara, shi ne ya lashe zaben da kashi 54 cikin 100. | ha |
Faransa da Amurka, da Tarayyar Kasashen Turai, da Tarayyar Kasashen Afirka duk sun bi sahun Majalisar Dinkin Duniya wajen amincewa da Alassane Ouattara a zaman zababben shugaban Ivory Coast, sun kuma yi kira ga Mr. Gbagbo da ya amince da wannan sakamako. | ha |
Tun da fari a jiya asabar din, shugaban majalisar zartaswar Kungiyar Tarayyar Turai, Jose Manuel barroso, ya bayyana Mr. Ouattara a zaman halaltaccen zababben shugaban Ivory Coast. | ha |
Asusun lamunin kudi na duniya, IMF, yace ba zai yi aiki da gwamnatin kasar Ivory Coast ba sai wadda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita. | ha |
Firayim ministan Ivory Coast, Guillaume Soro, wani tsohon madugun ‘yan tawaye da ya shiga gwamnatin hadin kan kasa da Mr. Gbagbo karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta 2007, ya fada jiya asabar cewa Alassane Ouattara shi ne zababben shugaban kasar. | ha |
Jiya asabar, sojoji sun kafa shingaye na tare hanyoyi a kewayen Abidjan, babban birnin kasar. Da ma dai kasar tana cikin dokar hana yawo, sannan an hana dukkan kafofin yada labarai na kasashen waje watsa labaransu a kasar. | ha |
Mazauna birnin Abidjan sun bayar da rahoton jin kararrakin harbe-harbe cikin dare a sassa dabam-dabam na birnin. Jiya asabar da rana, magoya bayan Mr. Ouattara sun fito kan tituna a rana ta biyu a jere su na kona tayu tare da kafa shingaye. Mutane 14 ne suka mutu ya zuwa yanzu a tashin hankalin siyasa. | ha |
Kotun Tsarin Mulki a Ivory Coast Ta Rusa Zaben Shugaban Kasar Da Hukumar abe Tace Shugaban 'Yan Hamayya Alassane Outtara ne Ya lashe | ha |
Hukumar Zabe A Ivory Coast Ta Ayyana Shugaban 'Yan Hamayya Ouattara A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Zagaye Na Biyu | ha |
Tsohon Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu Thabo Mbeki Yana Ivory Coast A kokarin Warware Rikicin Siyasar Kasar Da Yake Kara Tsanani. | ha |
'Yan Koriya Ta Kudu Na Ganin Za a Iya Cimma Zaman Lafiya A Taron Kolin Da Ake Shirin Yi Da Kim Jong Un | ha |
Daga shekara mai zuwa, mata zasu iya zuwa kallo a filayen wasanni uku a fadin kasar Saudiyya, a wani bangare na kokarin da daular keyi na fadada ‘yancin walwalar mata. | ha |
A watan da ya shige ne aka kyale daruruwan mata shiga wani filin wasa a birnin Riyadh, inda aka saba gudanar da wasan kwallon kafa, domin halartar wani bukin ranar ‘yancin kai na Sa’udiyya. | ha |
JIya lahadi, Hukumar Wasanni ta Kasa ta sanar ta kafofin Social Media cewa “ta fara shirye-shiryen gyara wasu filayen wasanni uku a Riyadh, da Jeddah da Dammam, ta yadda zasu iya karbar iyalai baki dayansu daga farkon shekarar 2018.” | ha |
Kasar Sa’udiyya mai akidar ra’ayin rikau, na daya daga cikin kasashen da suka fi takaita walwalar mata a bainar jama’a, kuma ta jima tana da dokokin da suka hana mata shiga filayen wasanni a saboda yadda ba a yarda mata su gauraya wuri guda da maza ba. | ha |
Wannan sanarwa ta biyo bayan wata guda a watan da ya shige wadda ta ce daga watan Yuni mai zuwa za a kyale mata su tuka mota. | ha |
Har ila yau, ana sa ran Sa’udiyya zata dage haramcin da ta kafa na gidajen sinima, kuma tana karfafa guiwar cudanyar maza da mata a lokacin bukukuwa, abinda ba a taba gani ba a tarihin kasar. | ha |
Najeriya na cewa dakarun sojin kasar sun sami nasarar hallaka wasu yan Boko Haram a karamar hukumar Madagali, jihar Adamawa, yayin da aka kashe wani dan yakin sa kai na maharba a artabun da suka yi. | ha |
Kamar yadda bayanai suka tabbatar,yan bindiga masu tada kayar bayan na Boko Haram sun gamu da ajalinsu lokacin da suke yunkurin kai wani harin sari-ka-noke, a yankin bakin Dutse,dake karamar hukumar Madagali,wanda ke kusa da dajin Sambisa. | ha |
Wani mazauni yankin yace yan yakin sakai na maharba ne suka soma yin artabu da wadannan yan Boko Haram a bakin dutsin da suka fafata har aka kashe wani dan sakai kodayake suma maharban sun sami nasarar kai wasu yan Boko Haram lahira. | ha |
A sanarwar da hedikwatar rundunan sojin Najeriya ta fitar dake dauke da sa hannun daraktan yada labarai na rundunan, Birgediya Janar Texas Chukwu,ta tabbatar da nasarar da aka samu kan mayakan na Boko Haram a yankin na Madagali. | ha |
Da yake karin haske shi ma Yusuf Muhammad shugaban karamar hukumar Madagali ya yaba da wannan sabon yunkuri. | ha |
Kamar yadda kididdiga ke nunawa rayuka da dama ne suka salwanta baya ga wadanda ke gudun hijira sanadiyar balahirar Boko Haram musamman a arewa maso gabashin Nigeria | ha |
Ziyarar jakadan Somaliya dake kasar Sin a jami'ar koyon harsunan ta waje ta Beijing - china radio international | ha |
Shiga Zaman Rayuwa Afirka a Yau Sin Ciki da Waje Amsoshin Tambayoyi Wasannin Motsa Jiki China ABC ::: TSOHO ::: | ha |
Jama'a barkannu da warhaka barkanmu da sake kasancewa a cikin wani sabon shirin na Sin da Afrika wanda ke zuwa muku daga sashen Hausa na gidan radiyon kasar Sin wato CRI. To a yau ma Maryam ce ke gabatar muku da shirin, to masu sauraro sai ku gyara zama domin jin yadda shirin zai kasance tare da ni Maryam daga nan sashen Hausa na CRI dake birnin Beijing. | ha |
A ranar 7 ga watan Disambar shekarar 2016 ne jakadan Somaliya a kasar Sin Yusuf Hassan Ibrahim, ya gabatar da wani muhimmin jawabi a lokacin da ya ziyarci jami'ar koyon harsunan kasashen waje ta Beijing dake nan kasar Sin wato BFSU. | ha |
A cikin jawabin da ya gabatar, jakadan ya tabo muhimman batutuwa game da tarihin dangantakar dake tsakanin Sin da kasar Somaliya. A cewarsa tun a shekarar 1960 ne aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, wato sama da shekaru 50 kenan da suka gabata, kuma Somaliya ce kasa ta farko a gabashin Afrika data fara kulla dangantaka da kasar Sin. | ha |
An tambayi jakadan game da wani yunkuri da jama'ar ta BFSU ta ke yi, na kirkiro sashen nazarin yaren kasar Somali, Ambasada Yusuf yace, yana goyon bayan wannan yunkuri, kuma yayi matukar farin ciki da jin wannan kyakkyawan labari. | ha |
Wakilin sashen Hausa na gidan radon CRI Ahmad Inuwa Fagam ya tattauna da jakadan game da batun dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Somaliya da kuma sauran batutuwa da suka shafi dangantakar Sin da kasashen Afrika, sai ya fara da tambayarsa ko yaya alakar dake tsakanin kasar ta Somaliya da makwabciyar ta kasar Kenya? Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance. | ha |
v Kokarin ta ya ba ta damar cimma burinta na wakiltar Tarayyar Najeriya gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu | ha |
Ningbo Newthink Motor Inc. ne kwararren manufacturer for DC / AC brushless Motors. Yana locates a Ningbo birni, da kuma maida hankali da wani yanki na 3,000 M2 da masana'antu. | ha |
Newthink Motor yana biya mai girma da hankali ga tabbacin inganci da kuma samfurin takardar shaida. A samar da tsananin bisa ga ISO9001-9004, kuma shi sun shũɗe AZ, ROHS, ETL, UL da dai sauransu. | ha |
Newthink motor kayayyaki da kuma ƙera high quality DC da AC brushless Motors zuwa biyan bukatar wani fanni na masana'antu da kuma janar aikace-aikace. Kamar mota, likita nema, gida nema, aikin lambu nema, ofishin aiki da kai, da kuma a kan haka. Muna da babban injiniya tawagar, da kuma iya siffanta daban-daban irin mota domin mu abokan ciniki. | ha |
Domin binciken game da kayayyakin mu, ko pricelist, don Allah ka bar adireshin imel mana da za mu zama a cikin touch cikin 24 hours. | ha |
Amurka za ta haramtawa wasu kasashe takwas na yankin Gabas ta Tsakiya da Kudancin Afirka, shiga jirage masu zuwa kasar da kayayyakin wuta irin su kwamfuta. | ha |
Wata majiya daga gwamnatin Amurka ta shaida wa BBC cewa, matakin zai shafi kamfanin jirage guda tara ne wadanda suke jigila a filayen jiragen saman kasar. | ha |
Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa, an dauki wannan mataki ne saboda bayanan sirri da aka samo daga wasu kasashe. | ha |
An kuma ruwaito cewa matakin zai hada ne da haramta shiga da kayayyaki kamar kwamfutoci da kyamarori da na'urar bidiyo ta DVD da na'urar yin gem, amma ban da wayoyi. | ha |
Hukumar kula da tsaron cikin gida ta Amurka, ta ki cewa komai a kan lamarin, amma ana sa ran za ta gabatar da jawabi a ranar Talata. | ha |
Har yanzu ba a fitar da jerin sunayen kamfanonin jiragen kasashen da matakin zai shafa ba, amma wani jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, lamarin zai shafi jiragen da ke tasowa daga filayen jirgi 10 ne daga kasashe takwas kamar haka: | ha |
Jami'ai sun ce matakin ba shi da ranar karewa. Kamfanin AP ya ruwaito cewa ba a sanar da kamfanin jiragen saman a hukumance ba har sai da misalin karfe bakwai na safiyar Talata agogon GMT. | ha |
Sai dai kamfanin jirgin sama na Jordan ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, zai haramtawa fasinjoji shiga jiragensa masu zuwa Arewacin Amurka da kayan lantarki, kamar yadda kafar yada labarai ta CNN ta fara ruwaitowa. | ha |
A watan Fabrairun 2016 ne bam ya fashe a wani jirgin kasar Dubai na kamfanin Daallo, jim kadan bayan tashinsa daga Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya. | ha |
Masu bincike sun ce wani fasinja ne ya shiga da wata kwamfuta mai dauke da bam. Matukin jirgin dai ya yi azamar tsayar da jirgin, kuma aka yi sa'a wanda ake zargi da shiga da bam din ne kawai ya mutu. | ha |
An yi hasashen cewa da a ce a lokacin da bam din ya fashe jirgin yana zura gudu ne a sararin samaniya, to da ba abin da zai hana jirgin tarwatsewa a sama. | ha |
Sai dai kuma da yake ana kaffa-kaffa kan abin da ya shafi bayanan sirri, jami'ai suna sanyi-sanyi wajen samo cikakken bayani a kan dalilin da ya sa Amurka ta gabatar da wannan sabon mataki. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. | ha |
Farashin danyan mai a kasuwannin duniya ya fadi da kasa da dala 35 kan kowacce ganga, faduwar da ba a taba gani ba cikin shekaru 11. | ha |
Bayan da kasuwarsa ta cushe a duniya, farashin danyen mai nau'in Brent a yanzu kashi daya ne cikin uku na yadda ake sayensa a tsakiyar 2014, duk kuwa da cewa ana zaman dardar a yankin Gabas ta tsakiya. | ha |
Maimakon haka sai farashin ya kara faduwa, a sakamakon hasashen da ake yi cewa kungiyar kasashe masu arzikin mai ta OPEC za ta amince ta rage yawan man da suke hakowa da nufin bunkasa farashinsa. | ha |
Maimakon hakan sabanin da kasashen ke ciki ba zai bari su amince a rage yawan man da ake fitarwa ba dan a kara fashinsa. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. | ha |
Image caption 'Yan wasan Panathinaikos sun yi wasa filin Apostolos Nikolaids kuma sun ci kofin gasar frimiya ta Girka har sau 20 | ha |
'Yan wasan kulob din Panathinaikos na kasar Girka sun fara yajin aiki saboda ba a biya su albashinsu na bara ba. | ha |
'Yan kwallon, wadanda suke jiran a biya su kudadensu na Disamba amma aka gaza yin hakan a 2018, sun fara yajin aikin ranar Litinin. | ha |
Sai dai kulob din ya shaida wa BBC cewa za a biya 'yan wasan kudadensu na watan Disamba ranar Alhamis kuma ana sa ran su dawo atisaye. | ha |
A makon da ya gabata, an kwace musu maki uku saboda sun kasa biyan tsohon 'dan wasan baya na Jamus Jens Wemmer bashin da ya ke binsu. | ha |
A makon da ya gabata, an ci tarar 'yan wasan Olympiakos Yuro 400,000 sannan shugaban kulob din ya neme su da su tafi hutu saboda rashin taka rawar gani. | ha |
Hakazalika a watan da ya gabata, an dakatar da shugaban Paok Salonika na shekara uku bayan da ya shigo fili da bindiga a lokacin da suke kara wa da AEK Athens. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. | ha |
Hukumar kwallon kafar nahiyar Turai ta yi garare-gyare a Gasar Zakarun Turai, wadda take gudanarwa, domin bunkasa wasannin. | ha |
Daga cikin gyare-gyaren, a yanzu an yarda dan kwallo ya buga wa sabuwar kungiyar da ta saye shi wasannin Gasar Champions League da ta Kofin Europa ko da a kakar ya buga wa tsohuwar kungiyarsa. | ha |
Sai dai dokar za ta fara aiki ne a kakar badi, lokacin an kammala gasar Champions League da ta Europa na bana. | ha |
Haka kuma hukumar ta amince a yi sauyin dan kwallo a karo na hudu a maimakon uku da ake yi yanzu, amma a wasannin zagaye na biyu a gasar, kuma sai an kai ga karin lokaci, idan kungiyoyin sun kammala minti 90 babu ci. | ha |
Saboda haka kungiyoyi za su rika bayyana 'yan wasa 23 a Champions League da Kofin Europa a maimakon 18, domin samun damar zabar dan kwallo na hudu da zai shiga karawar. | ha |
UEFA ta kuma ce za ta dinga gabatar da wadansu wasannin cikin rukuni da wuri wato da karfe 5.55 agogon GMT. | ha |
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka. | ha |
An zargi wata mace 'yar ƙasar Italiya da ƙaryar samun juna biyu, kuma ta je ta mai da jaririyar da ta saya, bayan ta gano cewa yarinyar ruwa biyu ne. | ha |
An kama matar tare da mahaifiyar jaririyar ta ainihi da kuma wani ɗan ƙasar Morocco da ake zargin shi ya haɗa cinikin. | ha |
Ba da goyon ciki a ƙasar Italiya, haramtaccen abu ne kuma akan ɗaure mutum a gidan yari a ci shi tara mai tsanani. | ha |
Rahotannin kafofin yaɗa labarai a Italiya sun ce abokin zamanta yana ɗaure a gidan yari kan laifin safarar ƙwaya, kuma a baya-bayan nan ta yi ɓari har sau biyu. | ha |
Mahaifiyar jaririyar, 'yar ƙasar Romaniya mai shekara 25, bayanai sun ce ta yi ciki ne bayan alaƙarsu da wani mutumin ƙasar Mali. | ha |
Lokacin da gano asalin jaririyar, sai uwar bogen ta ce lallai zai yi mata wahala ta iya yin bayani game da launin fatar yarinyar. | ha |
An fara nuna wasu-wasi ne farko a ofishin rijistar haihuwa na birnin Latina a kudancin Rome cikin watan Fabrairu, lokacin da wata mata ta nemi sanin yadda ake yi wa jaririn da aka haifa a gida rijista. | ha |
Bayan shafe lokaci, amma ba a je an yi rijistar ba, sai jami'ai suka sake tuntuɓa - sai dai an ce sai mai amsawar ta riƙa kwana-kwana. | ha |
Masu bincike sun gano jaririyar tana cikin ƙoshin lafiya, kuma mahaifinta na asali yana aiki ne a Rome. | ha |