text
stringlengths
101
6.99k
language
stringclasses
1 value
Kamar yanda akwai ayoyin da Malamai ke kafa hujja da su wurin kore ingancin saki uku a lokaci guda, mai neman cikakken bayani dangane da haka ya koma ga tafsirin aya ta 229 cikin Suratui Bakara.
ha
Kamar yanda bayanai suka gabata cewa wannan sura, an rada mata suna da surar saki ce sabili da tarin hukunce hukuncen saki wadanda shari'a ta wajabta da suke a cikinta, mai karatu ya karanta wasu daga irin wadannan hukunce hukunce, kamar wanda ya shafi yin iddar matar da aka yi mata sakin kome a gidan mijinta, da wajabcin ciyar da ita na tsawon lokacin da take cikin idda, kamar yanda saki ba a cikin tsarki ba, bai inganta ba wato dole ne sakin ya zamo ya auku ne cikin tsarkin da ba a sadu da ita a cikinsa ba haka nan ma mun karanta batun rashin ingancin sakin da aka yi shi ba gaban shaidu guda biyu adalai ba, kana kuma ya gabata magana kan cewa dukkannin sakin da aka yi shi da lafazin saki uku a lokaci guda, irin wannan saki ba a bakin komai yake ba face saki daya.
ha
Don haka muke ganin ya kamata a nan mu kawo cikon wasu sharudda wadanda idan har ba su tabbata ba, to saki babu yanda za a yi ya inganta a wajen Allah da Ma'aiki. Yana daga cikin irin wadannan sharuddan cewa shi saki dole ne a yi furuci da shi wato da za a yi shi a rubuce kadai ko kuma da ishara kadai ko hannunka mai sanda ga mutumin da ba bebe ko kurma ba, to a shari'a dai irin wadannan sakin ba su inganta ba.
ha
Kamar yanda mafi yawan malamai sun tafi a kan wajabcin furuci da saki ya kasance da siga kebantacciya wacce take da yaren larabci wato ita ce fadin mai saki ga matarsa: (Anti talikun)
ha
Sai dai kuma sun tafi kan cewa dukkan wanda ba zai iya kawo wannan furucin da yaren larabci ba, to zai iya yi da yaren da zai iya, kamar yanda mutumin da ya gaza yin furuci da saki, ko da kuwa shi ba kurma ko bebe ba ne a sakamakon wata larura, to irin wannan zai iya amfani da ishara ko rubutu gurin sakin matarsa duk da cewa an fi son rubutu a irin wannan halin.
ha
Wani daga sharuddan da saki ba ya inganta sai da shi, shi ne nufi wato wanda zai yi sakin ya zama ya kudurta cewa wannan kalma da yake furtawa ta saki yana nufin aiwatar da saki ne da ita, don haka mutumin da ya saki matarsa a halin yana maye ko kuma ba da niyyar yin saki ba, to sakin bai yi ba.
ha
Kamar yanda wanda ya furta saki a sakamakon takura da dole da aka yi masa, nan ma sakin daidai yake da sakin mahaukaci, wato ya bi ruwa.
ha
Wadannan su ne wasu daga cikin muhimman sharuddan da sai sun cika kafin saki ya inganta. Mai neman karin bayani yana iya komawa zuwa ga littattafan da suka yi bayani kan hukunce hukuncen aure da saki a mazhabar Ahlul Baiti (A.S.)
ha
Daya daga cikin abin da yake kawo tabarbarewan tarbiyya shi ne yawan samun rabuwar aure a cikin al'umma, duk da cewa shari'ar musulunci ta halatta yin saki a lokacin da ci gaba da rayuwar aure ta faskara ta yanda in har ba a rabu ba to dayansu ko dukkansu za su fada cikin wani hali na kaka ni kai, sai dai za ka samu cewa shari�a ta dauki matakin da ta kare mutane daga aukawa cikin hatsarin rabuwar aure ta hanyar sanya ka'idoji da iyakoki wadanda idan musulmi suka yi aiki da su, sai ka samu abu ne mai wahala wani ya saki matarsa kuma ta saku.
ha
Irin wadannan matakan wadanda shari'a ta yi amfani da su wurin kare mutane daga hadarin rabuwar aure su ne ake kira da hikimomin da suke kunshe cikin saki irin na sunna. Ga kadan daga cikinsu.
ha
Yana daga cikin irin wadannan hikimomi a wajabta wa mace zama a gidan mijinta bayan kuma ya sake ta har zuwa lokacin da za ta gama idda, muddun dai sakin ba ba'ini ba ne kamar yanda aka wajabta wa namiji ci gaba da rike ta a gidansa, da ciyar da ita da shayar da ita da tufatar da ita har tsayin lokacin da ta gama idda.
ha
Kamar yanda akwai ruwayoyin da suke dauke da bayanai kan yanda ya kamata matar da aka sake ta sakin kome, ta kasance kullum cikin ado, da sa turare kana da kyautata dabi'u wadanda za su jawo ran mijinta ya yi sanyi, ya kuma karkato hankalinsa zuma gare ta.
ha
An karbo daga Imam Bakir (A.S.) yana cewa: Matar da aka saki ya kamata a ce tana yin kunshi tana kuma rangada kwalli, kuma tana fesa turare, kana tana caba ado yanda ta ga dama, domin Allah Ta' ala yana cewa "ta yiwu bayan haka Allah ya haifar da wani abu (a tsakaninsu)" watakila shaukin mai da ita ya darsu a cikin zuciyarsa sai ka ga ya mai da ita.Wannan ruwayar ta zo cikin Tafsirus sakalain juzu'i na 5 shafi na 352.
ha
Wata hikimar kuma ita ce maganar a saki mace a cikin tsarkin da ba a kwanta da ita a cikinsa ba, ta yanda da za a yi sakin a halin an sadu da ita a cikin wannan tsarkin to sakin bai yi ba, wato dole ne a jira sai ta yi tsarki daga al'adanta. Wanda wannan jiran abu ne wanda zai iya taimakawa wajen hucewar fushin mijinta, ka ga sun dawo sun ci gaba da zaman lafiya a tsakaninsu.
ha
Kana yana daga cikin manya manyan hikimomin da ke hana saurin aukuwar rabuwar aure, maganar kafa shaidu biyu adalai, wadanda idan da za a yi saki babu su ko kuma babu daya daga cikinsu, to wannan sakin sam bai yi ba a shar'ance. Wannan magana ta shaidu biyu adalai ta magance mana matsalar sakin mata da tsakar dare, kamar yanda ko da an samu shaidu biyu matsawar ba su sifantu da sifa ta adalci ba ko kuma daya daga cikinsu ba adali ba ne shi ma dai saki bai yi ba.
ha
Kamar yanda kuma shari'a take kwadaitar da cewa ya kamata miji ya yi wa matar da ya saka, saki na sunna, (ya yi mata) ihsani wato ya kyautata mata kyautatawa su rabu cikin mutunci, wanda tasirin yin haka yana da yawan gaske, kadan daga cikin irin wannan tasiri shi ne yanda matar ba za ta kullace shi a ranta ba ta yanda idan akwai haihuwa a tsakaninsu, gaba da kiyayya ba za su faru ba sakamakon irin wannan rabuwa ta mutunci da suka�� yi.
ha
Idan kuma har ba 'ya'ya to zumunci ba zai rushe tsakanin danginta da dangin tsohon mijinta, wanda suka rabu cikin mutunci ba.
ha
A nan za mu so mu cike wannan binciken da wasu kalmomi na nasiha ga ma'aurata. Akwai tarin hadisai daga Ma'aiki (S.A.W.A.) wadanda ke yin horo ga miji da mata kan lizimtan tsabta da nesantar kazanta da duk wani abu wanda zai haifar da kyamar juna, kana da aikata dukkannin wani abu da zai jawo kauna da soyayya tsakaninsu, shin ta hanyar magana ne ko mu'amala ta hanyar ado ne ko kuma zuwa da abin dariya da nishadi a tsakaninsu.
ha
Wani abin takaici sai ka samu wasu maza suna yin nishadi a tsakanin abokan hirarsu amma da zarar sun iso soron gidan da iyalansu suke ciki take sai ka ga sun murtuke fuska, kana sun shiga kaurara murya wai su manya ne, alhali kuwa fiyayyen talikai, shugaban Manzanni Annabi Muhammad (S.A.W.A.) ga abin da yake fadi kan yanda ya kamata mu'amala ta kasance tsakanin miji da mata.Kana ya azurta shi ta inda bai yi tsammani ba, kuma duk wanda ya dogara ga Allah to shi (Allah) ya ishe shi, hakika Allah mai isar da al'amarinsa ne, lallai Ubangiji ya sanya wa kowane abu iyaka.
ha
Kuma wadanda suka yanke kauna daga yin haila cikin matayenku idan har kuka yi kokwanton (suna da ciki ko ba su da shi) to iddarsu wata uku ce, haka nan kuma matan da ba sa yin haila (su ma iddarsu wata uku ce), ma'abuta ciki kuma iddarsu ita ce haife cikinsu kana, wanda duk yaji tsoron Allah, (Allah) zai saukaka al'amarinsa.(3)
ha
Wadannan (hukunce hukuncen) umarnin Allah ne da ya saukar zuwa gare ku, kuma duk wanda ya ji tsoron Allah, to Allah zai kankare masa munanan ayyukansa kana ya girmama masa lada.(4)
ha
"Mafifici daga cikinku shi ne wanda ya fi kyautata wa iyalinsa kana ni na fi ku kyautata wa iyalina."(5)
ha
An karbo daga Imam Sadik (A.S.) yana cewa: "Hakika mata sun fita daga kame kansu zuwa ga yin lalata, ba komai ya sa suka auka zuwa ga lalata ba face karancin tsabtan mazajensu."
ha
Ku zaunar da su (wadannan mata da kuka saka) a inda kuke zaune gwargwadon karfm wadatarku, kada ku cutar da su domin ku takura musu (har su gudu daga gidan), (amma) idan sun kasance ma'abuta ciki to ku ciyar da su har [ sai sun haife cikinsu kana idan suka _ shayar muku da ('ya'yanku) to ku biya su ladan shayarwarsu, (sannan� dangane da dan da za'a shayar) ku yi kyakkyawar shawara wacce ta dace a tsakaninku, idan kuma har� (shawarar) ta ci tura, sai wata matar daban ta shayar masa da dan.(6)
ha
(Kana dangane da ciyar da wadanda �aka saka) Mawadaci lallai ya ciyar daga wadatar da yake da ita, duk �wanda kuma aka kuntata masa� arzikinsa (wato talaka) to lallai shi �ma ya ciyar daga abin da Allah ya ba �shi, Allah ba ya kallafa wa wani �bawa face gwargwadon ikon da ya ba shi, (domin) ba da dadewa ba �Allah zai kawo �sauki bayan tsanani.(7)
ha
�Akwai da yawa daga cikin birane da alkaryu wadan da mutanensu suka kangare wa umarnin Ubangijinsu da� manzanninsa sai muka yi musu hisabi matsananci kuma muka yi musu azaba ta ki .(8)
ha
(Asakamakon sabawar da suka yi wa umamin Ubangji sai allah ya tanadar musu azaba mai tsanani, (to don haka) ya ku masu hankalin da kuka yi imani kuji tsoron Allah, domin hakika Ubangiji ya saukar da abin da yake tunatarwa a gareku.(10)
ha
Ya aiko muku da Manzo, wanda yake karanta muku ayoyin Allah mabayyana don ya fitar da wadanda �suka yi imani kana suka yi aiki na gari daga nau'oin duhu zuwa ga haske duk wanda ya yi imani da Allah kana ya yi aiki na gari to Allah ��zai shigar da shi gidajen Aljanna��� I wadanda koramu ke gudana a karkashinsu, suna masu dauwama a cikinsu har abada, hakika (duk wanda ya shiga cikin Aljanna to) Allah ya kyautata masa arziki.(l 1)
ha
Allah shi ne wanda ya halicci sammai bakwai kana ya halicci kasa kwatankwacinsu (wanda kuma a ko da yaushe) umaminSa na sauka a tsakaninsu (sammai da kassai) don ku san cewa hakika Ubangiji mai iko ne kan kowane abu kana ku san cewa lallai ilimin Allah ya kewaye dukkan komai.(12)
ha
Firaministan kasar Sin ya jaddada bukatar kara bude kofa ga kasashen waje - china radio international
ha
Shiga Zaman Rayuwa Afirka a Yau Sin Ciki da Waje Amsoshin Tambayoyi Wasannin Motsa Jiki China ABC ::: TSOHO :::
ha
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada bukatar kara bude kofa ga kasashen waje don kara ciyar da shirin yin kwaskwarima gaba, da kara karfin kasuwa da inganta yanayin ci gaba.
ha
Li ya bayyana hakan ne a jiya Litinin yayin da ya kai ziyarar gani da ido ma'aikatar cinikayya da kuma babbar hukumar kwastan ta kasar. (Ibrahim)
ha
v Kasar Sin ta fitar da dokokin bude bangaren sayar da takardun hada-hadar kudi ga baki masu sha'awar zuba jari 2018-04-29 16:56:03
ha
v Sin ta dauki matakan kara habaka bude kofa ga kasashen ketare ne da nufin sada kasashe daban daban da moriyar saurin ci gabanta 2018-04-12 19:45:24
ha
v Tsarin bude kofa na kasar Sin ya samarwa nahiyar Afrika wata hanya ta samun cigaban harkokin zamani 2018-03-12 10:48:48
ha
v Birnin Huzhou na lardin Zhejiang na kasar Sin na dukufa kan aikin kiyaye muhalli yayin samun ci gaba
ha
Hukumomi a Najeriya sun ce sun dakile wasu masu safarar mutane tare da ceto yara 10 wadanda ake son kai wa Moscow da sunan zuwa kallon gasar kofin duniya.
ha
Gwamnatin Najeriyar ta yi gargadin cewar masu laifi suna amfani da gasar cin kofin duniya domin samun takardar shiga ga yara kanana wadanda masu safarar mutane za su yi amfani da su ta hnayar da bai dace ba.
ha
Yara mata tara da kuma yaro namiji daya suna dab da shiga jirgin sama na kamfanin jiragen sama na Turkiyya ne daga Legas zuwa Moscow, a lokacin da jami’an hukumar da ke yaki da fataucin mutane (NAPTIP) su ka ceto su.
ha
An kama mutum biyar da ake zargi, ciki har da dan sanda daya da kuma wani jami’in wajen fitar da yaran.
ha
An bai wa yaran fasfo da kuma takardar shaida na masu goyon bayan ‘yan kwallo a filin jirgin, domin a dauke su tamkar masoya kwallon kafa ne masu son tafiya Rasha kallon gasar kwallon kafar ta duniya.
ha
Mai yiwuwa ne bayan sun kai isa kasar, za a kai su wasu kasashen daban inda masu safarar mutanen ke da abokai wadanda za su tilasta musu yin aiki.
ha
Hausa: Mu, (duk abin da yake) ne, a cikin rãyuwar lokacin daya, guda, kai babu shi kasancewa daga m sani
ha
Katafaren Kamfanin kera motocin Toyota na Japan ya bukaci a janye motoci fiye da miliyan biyu saboda matsala a jakar iska mai rage tasiri hatsari.
ha
An samu matsalar ce a samfurin motocin Toyota kimanin 20, ciki harda kirar Corolla Sedan da Toyota Yaris 'yar kumbula.
ha
Wani mai magana da yawun Toyota ya ce babu wanda ya jikkata ko ya samu hatsari sakamakon matsalar jakar iskar.
ha
A cikin watan Afrilu ne Toyota ya kira a maida motoci kimanin miliyan shida da rabi don gyara matsalar da suke da ita ciki har da jakunkunan da iska da ba ta hura su idan an samu hatsari, da matsalar da ta shafi kujeru da sitiyari da makunnin motoci.
ha
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka
ha
Cibiyar Chatham House da ke Birtaniya ta ce amfani da karfin soji shi ne ya kara janyo tabarbarewar rikicin Boko Haram a Najeriya maimakon magance shi.
ha
A rahoton kungiyar mai gudanar da bincike da shirya mahawara kan harkokin cigaban kasashe, ta ce, matakin sojin ya harzuka 'yan kungiyar ne kawai.
ha
Farfesa Marc-Anthoine na wata jami'a a Paris wanda ya gudanar da binciken, ya ce wannan mataki shi ya sa 'yan Boko Haram din suke kai hari kan kowa da kowa, sabanin yadda suke da farko.
ha
Amma kuma ya zargi gwamnatin kasar da rashin rungumar tattaunawa da 'yan kungiyar tsakani da Allah, domin kawo karshen matsalar.
ha
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka
ha
Wasu daga cikin kyawawan hotuna daganahiyar Afirka da kuma na 'yan Afirka dake zaune a wasu sassan duniya a makon da ya gabata.
ha
Wadansu Kiristoci yayin wani bikin Meskel na addinin Kirista a babban birnin kasar Habasha, Addis Ababa.
ha
Wata mata 'yar kasar Senegal tsugune a gaban wani kabari ranar Talata yayin cika shekara 15 da nutsewar wani jirgin ruwa mai suna Joola.
ha
Akalla mutum 1,800 suka mutu lokacin da jirgin ruwan ya nutse a shekarar 2002, adadin ya zarta na wadanda suka mutu lokacin da jirgin ruwan Titanic ya yi hadari a shekarar 1912.
ha
Wata mata tana kallon wadansu kayayyaki da aka baje kolinsu a wani bikin baje koli mafi girma na zamani a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu.
ha
Wani limanin Kirista Evan Mawarire rike da tutar kasar Zimbawea lokacin da 'yan sanda suka tasa keyarsa zuwa caji ofis ranar Talata. Ana tuhumar Fasto Mawarire da laifin sukar gwmanati Shugaba Robert Mugabe kan hanyoyin da take bi wajen shawo kan matsalar tattalin arzikin kasar.
ha
Wani mutum lokacin da yake wanke goro a birnin Anyama na kasar Kwaddibuwa ranar Litinin. Kwaddibuwa ita ce kasa ta biyu da take kan gaba wajen samar da goro.
ha
Wadansu mata suna jan akalar rakuma lokacin da Shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya kai ziyara garin Umm al-Qura na yankin Darfur a makon jiya.
ha
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka
ha
Shekarar 2016 na cikin shekarun da masu ruwa da tsaki a fina-finan Hausa, wato Kannywood ba za su manta da ita ba.
ha
Abubuwa da dama sun faru a shekarar — masu dadi da marasa dadi — wadanda suka yi tasiri kan yadda ake tafiyar da wannan babbar harka.
ha
Tun a farkon shekarar ne, wato a watan Fabrairu, Kannywood ta soma samun babban gibi sakamakon mutuwar fitacciyar jarumar nan Aisha Dankano.
ha
Aisha — wacce aka fi sani da Sima - ta yi fice wajen amfani da kalmomi masu cike da hikima da kuma ban-dariya a fina-finan Hausa, wadanda da wuya a samu wanda ko wadda za ta maye gurbinta a wannan bangare.
ha
Al'amura sun ci gaba da tafiya kamar yadda suka kamata a Kannywood, inda aka rika sa ran fitar da manya manyan fina-finai kamar su Basaja Gidan Yari, har watan Yuni lokacin da batun gina katafariyar alkaryar fina-finai ya taso.
ha
A wancan lokacin, shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma'ila Na'abba Afakallah, ya shaida min cewa alkaryar za ta kasance ta farko a Najeriya, yana mai cewa masu shirya fina-finai daga kowacce kusurwa ta duniya za su iya zuwa Kano domin yin amfani da ita.
ha
A cewarsa "Za a kashe sama da Naira biliyan uku wajen gina alkaryar, kuma ana sa ran fiye da mutum 10,000 za su samu aiki idan aka kammala aikin."
ha
Sai dai nan da nan wannan batu ya jawo ce-ce-ku-ce kuma muhawarar da aka rika tafkawa a shafukan sada zumunta na zamani a kan dacewa ko rashin dacewar gina alkaryar da kuma caccakar da shirin ya sha a wajen wasu Malamai sun tilasta wa gwamnatin tarayya soke shi.
ha
Tun bayan da gwamnatin tarayya ta soke shirin gina alkaryar fina-finai ne dai aka rika yin musayar yawu a tsakanin wasu 'yan fim da malamai, inda aka ambato wasu malaman na cewa wasu 'yan fim din 'yan luwadi ne, yayin da wasu 'yan fim din suka rika yin gugar-zana ga malaman.
ha
Sai dai da alama batun zargin luwadin da aka yi wa 'yan Kannywood din ya shiga kunnen jama'a, lamarin da ya harzuka 'yan fim din.
ha
A wata hira da fitaccen jarumi Adam A. Zango ya yi da gidan talabijin na DITV da ke Kaduna, ya musanta zargin yin luwadi.
ha
Jarumin ya dafa Al-Qur'ani, sannan ya sha rantsuwa cewa bai taba yin luwadi ba, kuma shi ma ba a taba yi da shi ba, yana mai cewa idan har kalamansa babu gaskiya a ciki, Allah "ya halaka ni".
ha
Ya kara da cewa, "Wallahil azimun! Wallahil azimun ni ban taba luwadi ba, kuma ba a taba luwadi da ni ba!"
ha
Abokin aikinsa ma, Mustapha Badamasi, wanda aka fi sani da Naburaska, ya caccaki mutanen da suke yi musu kazafi, yana mai cewa nan gaba kadan zai fito da shaidun da za su tozarta mutanen.
ha
Masu nazari a harkar fina-finan Hausa sun yi ittifaki cewa rabon da Kannywood ta shiga rikici kamar wanda Rahama Sadau ta janyo mata tun bayan faifan bidiyon tsaraicin Maryam Hiyana da ya fita a shekarun baya.
ha
A watan Satumba ne Rahama ta fito a waƙa salon hip hop mai suna I Love You tare da mawakin nan Classiq, wacce ke da tsawon minti hudu da dakika 19.
ha
A wurare da dama an nuna ta tana jingina a jikin Classiq, lamarin da ya jawo zazzafar muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki na Kannywood da ma al'uma.
ha
Hakan dai ya sa kungiyar masu harkar shirya fina-finan Hausa, MOPPAN, ta sanar da korar ta daga Kannywood.
ha
Jarumar ta nemi gafara kan wannan batu kodayake ta ce ba zai yiwu ta yi aiki ba tare da "na taɓa wani ba".
ha
Wani abu da ba za a manta da shi a wannan shekarar game da 'yan Kannywood ba shi ne yadda wasunsu suka mayar da hankali wajen taimakawa jama'a ta hanyar kafa gidauniya.
ha
Jarumai irinsu Adam A. Zango da Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon sun kafa gidauniyoyi domin abin da Gabon ta bayyana da cewa "nuna godiya ga Allah bisa baiwar da ya yi mana, sannan mu nunawa marasa karfi cewa Allah yana tare da su."
ha
Ita dai wannan jaruma ta bayar da tallafi sau da dama ga 'yan gudun hijirar da suka bar gidajensu sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram, wadanda yanzu haka suke sansanonin 'yan gudun hijira.
ha
A cewar jarumin, gidauniyar za ta rika bayar da taimako ga marasa galihu da marasa lafiya da 'yan gudun hijira da marayu da zawarawa.
ha
Zango ya ce zai samu kudin gudanar da gidauniyar ne ta hanyar shirya bukukuwan rawa a dukkan jihohin Najeriya wanda zai soma a watan Janairu mai zuwa.
ha
Ita ma Nafisa Abdullahi ta kafa irin wannan gidauniya mai suna The Love Laugh Foundation, wacce ta ce za ta mayar da hankali ne kan nuna kauna da tallafi ga marasa galihu da mata da marayu da 'yan gudun hijira.
ha
Masana abubuwan da ke faruwa a Kannywood sun yi san-barka ga wannan kokari da jaruman ke yi na taimaka wa al'uma.
ha
Malam Ibrahim Sheme, wanda ya dade yana tsokaci kan Kanyywood, ya ce matakin zai inganta dangantakar da ke tsakanin jaruman da al'umar da ke yi musu kallo a matsayin masu wargaza tarbiyya.
ha
Ya kara da cewa, "Wannan mataki yana da kyau amma ina ganin ba shi da tsari. Ya kamata jarumai kamar goma wadanda ke da irin wannan aniya su hada kungiya da za ta rika aiwatar da irin wannan shiri, ba kowa ya yi gaban kansa ba."
ha
A yayin da muke bankwana da shekarar 2016 kuma muke shirin shiga sabuwar shekara, babu makawa cewa harkokin da ake gudanarwa a Kannywood za su ci gaba da jan hankalin jama'a da kuma yin tasiri a rayuwarsu.
ha
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka.
ha
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bai wa Nigeria daga nan zuwa Juma'a cewar ta janye hukuncin da wata babbar kotu a Jos ta yanke na rushe zaben NFF ko kuma ta hukunta ta.
ha
A wata wasika da FIFA ta rubuta wa Nigeria ranar Talata ta bukaci kasar da ta bi umarnin da ta ba ta kafin 31 ga watan Oktoba.
ha
FIFA ta bukaci a mayar da Shugabancin hukumar NFF wanda zaben 30 ga watan Satumba ya dora Amaju Pinnick a matsayin shugaban kwallon kafar kasar.
ha
Hukuncin da FIFA za ta dauka kan Nigeria zai hada da dakatar da ita shiga duk wata harkar kwallon kafa a duniya.
ha
Hakan kuma zai iya hana Nigeria shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka, idan ta samu gurbin buga gasar wadda take rike da kofin.
ha
A shekarar nan sau biyu FIFA tana dakatar da Nigeria shiga harkar kwallon kafa, ta kuma gargade ta da kada a sake samun rikici a hukumar.
ha
Copyright © 2018 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abin da ke kunshi a wasu shafukan na daban ba. Karanta tsarinmu game da bakin shafuka.
ha